18 “Babu tsoron Allah a cikin sha'aninsu sam.”
18 “Babu tsoron Allah a idanunsu.”
Zunubi yakan yi magana da mugun daga can gindin zuciyarsa, Yakan ƙi Allah, ba ya jin tsoronsa.
Kada ka yi ƙyashin masu aikata zunubi tsoron Ubangiji kaɗai za ka sa a gaba.
Ka zama mai biyayya da aminci, Allah kuwa zai gafarta maka zunubinka. Ka dogara ga Ubangiji, ba wani mugun abu da zai same ka.
Ƙin mugunta shi ne tsoron Ubangiji, Na ƙi girmankai, da fāriya, da mugayen hanyoyi, Da maganganu na ƙarya.
Sai aka ji wata murya daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, ya ku bayinsa, Ku da kuke jin tsoronsa, yaro da babba.”
Amma ɗayan ya amsa, ya kwaɓe shi, ya ce, “Kai ko tsoron Allah ma ba ka yi, kai, da yake hukuncinka daidai da nasa?
Ibrahim ya ce, “Na yi haka, domin ina zaton babu tsoron Allah ko kaɗan a wannan wuri, shi ya sa na zaci, kashe ni za a yi saboda matata.
Yadda suka yi muku kwanto a hanya, suka fāɗa muku ta baya, suka karkashe waɗanda suka gaji tiɓis. Ba su ko ji tsoron Allah ba.
Ba su kuma san hanyar salama ba.”