Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.
Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.
“Domin haka ni Ubangiji Allah zan hukunta ku, ku mutanen Isra'ila, kowa gwargwadon ayyukansa. Ku tuba, ku bar laifofinku domin kada su zama muku dalilin halaka.
Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.
Mai yiwuwa ne ka ce kai ba ruwanka, amma Allah ya sani, yana kuwa auna manufofinka. Yana lura da kai, ya kuwa sani. Yakan sāka wa mutane a kan abin da suke aikatawa.
Kana da bangaskiya? To, ka riƙe ta tsakaninka da Allah. Albarka tā tabbata ga wanda zuciyarsa ba ta ba shi laifi ba, a game da abin da hankalinsa ya ga daidai ne.
Yanzu fa, sai ka tafi, ka bi da mutanen zuwa wurin da zan faɗa maka, ga shi, mala'ikana zai wuce gabanka. Duk da haka a ranar da zan waiwaye ku, zan hukunta su saboda zunubinsu.”