Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 2:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ya kai mutum, kai da kake ganin laifin masu yin haka, alhali kuwa kai kanka, kana yinsu, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Saboda haka sa’ad da kai mutum kurum, kana ba su laifi, duk da haka kana aikata abubuwan nan, kana tsammani za ka tsere wa hukuncin Allah ne?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 2:3
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji yana ƙin kowane mutum da yake fariya. Irin wannan mutum ba zai kuɓuta daga hukunci ba.


Waɗannan kuwa ko da yake sun san shari'ar Allah cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, sun cancanci mutuwa, duk da haka, ba aikata su kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon masu yinsu.


Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira.


Amma Yesu ya ce masa, “Haba kai kuwa, wa ya sa ni in zama muku alƙali, ko in raba muku gādo?”


Bayan ɗan lokaci kaɗan kuma, sai wani ya gan shi, ya ce, “Kai ma, ai, ɗayansu ne.” Amma Bitrus ya ce, “Ya mutum, ba haka ba ne.”


Kuna tsammani ba ni da ikon neman taimako gun Ubana ba, nan da nan kuwa ya aiko mini fiye da rundunar mala'iku goma sha biyu?


Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?


Ya ce, “Ya kai, mutumin da ake sonka ƙwarai, kada ka ji tsoro, salama a gare ka, ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali!” Sa'ad da ya yi magana da ni, na sami ƙarfi na ce, “Yanzu sai shugabana ya yi magana, ka sa na sami ƙarfi.”


Bai kuwa cika rantsuwarsa da alkawarinsa ba. Ya ƙulla alkawari, amma ga shi, ya aikata dukan waɗannan abubuwa, ba zai kuɓuta ba.


Amma Sarkin Yahuza ya tayar masa, da ya aiki wakilai zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. To, zai yi nasara? Wanda ya yi irin wannan abu zai tsira? Zai iya ta da alkawari sa'an nan ya tsere?


Ka tabbata fa za a hukunta mugaye, amma ba za a hukunta adalai ba.


Kun aikata waɗannan duka, ni kuwa ban ce kome ba, Saboda haka kuka zaci ni kamar ku nake. Amma yanzu zan tsauta muku, In bayyana muku al'amarin a fili.


“Ayuba, ba daidai ba ne, ka ce, Ba ka yi laifi a gaban Allah ba,


sai hakiman Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama tsohonka ne, da ya aiko manzanninsa su yi maka ta'aziyya? Ai, manzannin nan da ya aiko 'yan leƙen asirin ƙasa ne. Sun zo ne su bincika don su san yadda za a ci birnin.”


Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?


to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji kansa, shi ne ya fara sanar da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi,


Amma Bitrus ya ce, “Haba, ban ma san abin da kake faɗa ba.” Nan take, kafin ya rufe baki, sai zakara ya yi cara.


Ka hukunta su, ya Allah saboda muguntarsu, Da fushinka ka kori waɗannan mutane!


Saboda haka ba ka da wata hujja, kai mutum, ko kai wane ne da kake ganin laifin wani. A yayin da kake ganin laifin wani, ai, kanka kake hukunta wa, don ga shi, kai mai ganin laifin wani, kai ma haka kake yi.


Mun dai san hukuncin Allah a kan masu yin haka daidai ne.


Ya kai ɗan adam! Wane ne kai har da za ka yi jayayya da Allah? Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa magininsa, “Don me ka yi ni haka?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ