Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 16:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, 'yan'uwana, abokan ɗaurina, waɗanda suke shahararru a cikin manzanni, har ma sun riga ni bin Almasihu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka daure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 16:7
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Timoti, abokin aikina, yana gaishe ku, haka kuma Lukiyas da Yason da kuma Susibataras, 'yan'uwana.


Ku gai da 'dan'uwana Hirudiyan. Ku gai da waɗanda suke na Ubangiji a cikin jama'ar Narkisas.


Abafaras, abokin ɗaurina saboda Almasihu Yesu, yana gaishe ka,


Aristarkus, abokin ɗaurina, yana gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnaba. Shi ne aka riga aka yi muku umarni a game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe shi.


Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.


Amma kuwa ikilisiyoyin Almasihu da suke a ƙasar Yahudiya, ba su san ni ido da ido ba tukuna.


Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ne, tsohon al'amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo.


Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.


Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.


Ta haka muka sani muna a zaune a cikinsa, shi kuma a cikinmu, saboda Ruhunsa da ya ba mu.


Kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba, sai dai sabuwar halitta ita ce wani abu.


In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.


Waɗanda kuma aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne (ko su wane ne, ai, duk ɗaya ne a guna, domin Allah ba ya tāra), ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙare ni da kome ba.


In su bayin Almasihu ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan ɗauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri iri.


Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.


Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu.


Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa.


A ran nan ne fa za ku sani, ni cikin Uba nake, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku.


Duk wanda suke cin naman jikina, yake shan jinina, a cikina yake zaune, ni kuma a cikinsa.


Ni Ubangiji, zan kuɓutar da dukan zuriyar Yakubu, Za su kuwa yi yabona.”


Amma Ubangiji ya ceci Isra'ila, Nasararsa kuwa za ta tabbata har abada, Mutanensa ba za su taɓa shan kunya ba.


Da umarnin wahayi ne na tafi, har na rattaba musu bisharar da nake yi a cikin al'ummai, amma a keɓance a gaban waɗansu shugabannin ikkilisiya, kada himmar da nake yi, ko wadda na riga na yi, ta zamana ta banza ce.


In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.


Da ma a la'ance ni, a raba ni da Almasihu saboda dangina, 'yan'uwana na kabila!


Ku gai da Bilkisu da Akila, abokan aikina a cikin Almasihu Yesu,


Ku gai da Maryamu, wadda ta yi muku aiki ƙwarai da gaske.


Ku gai da Amfiliyas, ƙaunataccena a cikin Ubangiji.


Ku gai da Urbanas abokin aikinmu a cikin Almasihu, da kuma ƙaunataccena Istakis.


Ku kuma gai da Abalis, amintaccen nan a cikin Almasihu. Ku gai da jama'ar Aristobulus.


Na san wani mutum wanda yau shekara goma sha huɗu ke nan, aka ɗauke shi zuwa Sama ta uku bisa ga ikon Almasihu, ko yana a cikin jiki ne, ko ba a cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ne masani.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ