6 Ku gai da Maryamu, wadda ta yi muku aiki ƙwarai da gaske.
6 Ku gai da Maryamu wadda ta yi muku aiki tuƙuru.
wadda ake yabo a kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi 'ya'ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke ƙafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari.
Ku gai da Tarafina da Tarafusa, masu aikin Ubangiji. Ku gai da Barsisa, ƙaunatacciya, wadda ta yi aikin Ubangiji ƙwarai da gaske.
Akwai kuma waɗansu mata da yawa a can suna hange daga nesa, waɗanda suka biyo Yesu tun daga ƙasar Galili, suna yi masa hidima.
In kuwa 'yan'uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al'ummai ma ba haka suke yi ba?
Ku kuma gai da ikilisiyar da take taruwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccena Abainitas, wanda yake shi ne ya fara bin Almasihu a ƙasar Asiya.
Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, 'yan'uwana, abokan ɗaurina, waɗanda suke shahararru a cikin manzanni, har ma sun riga ni bin Almasihu.
Amma muna roƙonku 'yan'uwa, ku girmama masu fama da aiki a cikinku, wato waɗanda suke shugabanninku cikin Ubangiji, suke kuma yi muku gargaɗi.