Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 16:4 - Littafi Mai Tsarki

4 waɗanda suka kasai da ransu saboda ni, ba kuwa ni kaɗai nake gode musu ba, har ma da dukkan ikilisiyoyin al'ummai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sun yi kasai da ransu saboda ni. Ba ni kaɗai nake musu godiya ba amma har ma da dukan ikkilisiyoyin Al’ummai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 16:4
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, ta wurin ba da ransa da ya yi saboda mu. Mu kuma ya kamata mu ba da ranmu saboda 'yan'uwa.


domin ya kusa ya mutu saboda aikin Almasihu, yana sai da ransa domin ya cikasa ɗawainiyarku gare ni.


'Yan'uwa, ku ne kuka zama masu koyi da ikilisiyoyin Allah da suke na Almasihu Yesu, waɗanda suke a ƙasar Yahudiya, don ku ma kun sha wuya a hannun mutanen ƙasarku, kamar yadda ikilisiyoyin nan ma suka sha a hannun Yahudawa,


To, a yanzu kuma ga zancen ba da gudunmawa ga tsarkaka, kamar yadda na umarci ikilisiyoyin Galatiya, haka ku ma za ku yi.


Sai dai kowa yă yi zaman da Ubangiji ya sa masa, wanda kuma Allah ya kira shi a kai. Haka nake umarni a dukan Ikilisiyoyi.


Da ƙyar za a sami wanda zai ba da ransa, saboda mutum mai adalci, ko da yake watakila saboda mutum mai nagarta wani ma sai yă yi kasai da ransa.


Ta haka ikilisiyoyi suka ƙarfafa a cikin bangaskiya, a kowace rana suna ƙara yawa.


Bulus ya zazzaga ƙasar Suriya da ta Kilikiya, yana ta ƙarfafa Ikilisiyoyi.


Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa.


Domin haka Ubangiji ya ce, Ga shi, yana shirya wa wannan jama'a masifa, Wadda ba za ku iya kuɓuta daga cikinta ba. Ba kuma za ku yi tafiyar alfarma ba, Gama mugun lokaci ne.


Ka sa abokan gābana su gudu daga gabana, Na hallaka waɗanda suke ƙina.


Da suka kawo sarakunan a wurin Joshuwa, sai Joshuwa ya kirawo dukan Isra'ilawa, sa'an nan ya ce wa shugabannin mayaƙa, waɗanda suka tafi tare da shi, “Ku matso kusa, ku taka wuyan sarakunan nan.” Suka kuwa zo kusa, suka taka wuyansu.


Daga Yahaya zuwa ga ikilisiyoyin nan bakwai da suke a ƙasar Asiya. Alheri da salama su tabbata a gare ku daga wanda yake a yanzu, shi ne a dā, shi ne kuma a nan gaba, da kuma Ruhohin nan bakwai da suke a gaban kursiyinsa,


Sa'an nan ne Ikkilisiyar duk ƙasar Yahudiya, da ta Galili, da ta Samariya ta sami lafiya, ta ingantu sosai, suna tafiyar da al'amuransu da tsoron Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki na taimakonsu, har suka yawaita.


waɗanda suka sayar da ransu saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Ku gai da Bilkisu da Akila, abokan aikina a cikin Almasihu Yesu,


Ku kuma gai da ikilisiyar da take taruwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccena Abainitas, wanda yake shi ne ya fara bin Almasihu a ƙasar Asiya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ