Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 16:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Amma ku kam, ai, kowa ya san biyayyarku, shi ya sa nake farin ciki da ku. Sai dai ina so ku gwanance da abin da yake nagari, amma ya zama ba ruwanku da mugunta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Kowa ya riga ya ji game da biyayyarku, don haka ina cike da farin ciki game da ku; amma ina so ku zama masu hikima game da abin da yake nagari, ku kuma zama marasa laifi ga abin da yake mugu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 16:19
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ga shi, na aike ku kamar tumaki a tsakiyar kyarketai. Don haka sai ku zama masu azanci kamar macizai, da kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.


Ya ku 'yan'uwa, kada ku yi hankali irin na yara, sai dai a wajen mugunta, ku yi halin jarirai, amma a wajen hankali ku yi dattako.


don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,


Da farko dai ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko'ina a duniya.


Addu'ata ita ce, ƙaunarku ta riƙa haɓaka da sani da matuƙar ganewa,


Ubangiji ya ce, “Mutanena wawaye ne, Ba su san ni ba, Yara ne dakikai, Ba su da ganewa. Suna gwanance da aikin mugunta, Amma ba su san yadda za su yi nagarta ba.”


Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.


Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da yake nufin Ubangiji.


Abin da nake yi ba zai zama laifi ba, Yaushe za ka zo wurina? Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.


To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar 'yan tumaki a tsakiyar kyarketai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ