Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 16:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Ku kuma gai da Abalis, amintaccen nan a cikin Almasihu. Ku gai da jama'ar Aristobulus.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ku gai da Afelles wanda amincinsa cikin Kiristi tabbatacce ne. Ku gai da iyalin gidan Aristobulus.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 16:10
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wanda duk yake bauta wa Almasihu ta haka, abin karɓa ne ga Allah, yardajje ne kuma ga mutane.


Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne (wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan jarraba ta da wuta), domin bangaskiyar nan taku tă jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Almasihu.


Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.


Sai an gwada su tukuna, in kuma an tabbata ba su da wani abin zargi, to, sai su kama aikin hidimar.


Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.


Muna kuma aiko da ɗan'uwanmu tare da su, wanda sau da yawa muka tabbatar da himma tasa ta hanya iri iri, yanzu kuma ya fi koyaushe himma, domin amincewa da ku da yake yi ƙwarai da gaske.


Na rubuto muku wannan takanas, domin in jarraba ku, in ga ko kuna yin biyayya ta kowace hanya.


Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.


Ka gayar mini da Bilkisu da Akila, da mutanen gidan Onisifaras.


In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.


Ku gai da Bilkisu da Akila, abokan aikina a cikin Almasihu Yesu,


Ku gai da Andaranikas da Yuniyas, 'yan'uwana, abokan ɗaurina, waɗanda suke shahararru a cikin manzanni, har ma sun riga ni bin Almasihu.


Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ne, tsohon al'amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo.


Na san wani mutum wanda yau shekara goma sha huɗu ke nan, aka ɗauke shi zuwa Sama ta uku bisa ga ikon Almasihu, ko yana a cikin jiki ne, ko ba a cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ne masani.


Amma kuwa ikilisiyoyin Almasihu da suke a ƙasar Yahudiya, ba su san ni ido da ido ba tukuna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ