Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku.
Abin da kuka koya, kuka yi na'am da shi, abin kuma da kuka ji kuka gani a gare ni, sai ku aikata. Ta haka Allah mai zartar da salama zai kasance tare da ku.
Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari,