Saboda haka ne zukatanmu suka ƙarfafa. Banda ƙarfafa zukatanmu kuma, har wa yau mun ƙara farin ciki ƙwarai, saboda farin cikin Titus, don dukanku kun wartsakar da shi.
Da aka shirya mu tashin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da waɗansu 'yan sarƙa a hannun wani jarumi, mai suna Yuliyas, na ƙungiyar Augustas.