Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 15:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Ya 'yan'uwana, ni ma da kaina na amince da ku, cewa ku da kanku masu nagarta ne ƙwarai da gaske, masu cikakken sani, kun kuma isa ku gargaɗi juna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Ni kaina na tabbata, ’yan’uwana, cewa ku kanku kuna cike da kirki, cikakku cikin sani da kuma ƙwararru don yin wa juna gargaɗi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 15:14
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don haka, lalle kullum ba zan fasa yi muku tunin waɗannan abubuwa ba, ko da yake kun san su, kun kuma kahu a kan gaskiyar nan da kuke da ita.


Ina rubuto muku, ba don ba ku san gaskiya ba ne, a'a, sai domin kun san ta, kun kuma sani gaskiya ba ta haifar ƙarya.


To, yanzu a game da abubuwan da aka yanka wa gumaka, mun sani dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kumbura mutum, ƙauna kuwa takan inganta shi.


Saboda haka, sai ku ƙarfafa wa juna zuciya, kuna riƙa inganta juna, kamar dai yadda kuke yi.


Maganar Almasihu tă kahu a cikin zuciyarku a yalwace, kuna koya wa juna, kuna yi wa juna gargaɗi da matuƙar hikima ta wurin rairar waƙoƙin Zabura da na yabon Allah, kuna kuma raira waƙa ga Allah, kuna gode masa tun daga zuci.


Amma in wani mutum, wanda yake da rarraunan lamiri, ya gan ka, kai da kake da sani, kana ci a ɗakin gunki, ashe, wannan ba zai ƙarfafa lamirinsa har ya ci abincin da aka miƙa wa gunki ba?


Amma dai ba kowa ne yake da wannan sani ba. Amma waɗansu ta wurin sabawarsu da al'amuran gunki har yanzu, sukan ci naman da suka ɗauka kamar an yanka wa gunki ne. Saboda haka lamirinsu, da yake rarrauna ne, ya ƙazantu.


har ta kowace hanya aka wadata ku a cikinsa, a wajen yin magana duka da ilimi duka,


Don na tabbatar da biyayyarka, shi ya sa na rubuto maka, don na sani za ka yi, har fiye da abin da na faɗa.


Muna kuma yi muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa.


domin haske shi ne yake haifar duk abin da yake nagari, na adalci, da na gaskiya.


Ko da yake mun faɗi haka, a game da ku kam, ya ƙaunatattu, mun tabbata kuna a kan abubuwa mafiya kyau na zancen ceto.


Ko da yake kamar a yanzu kam, ai, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sāke koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba, har ya zamana sai an ba ku nono, ba abinci mai tauri ba.


Ina tunawa da sahihiyar bangaskiyarka, wadda da farko take tare da kakarka Loyis, da mahaifiyarka Afiniki, a yanzu kuma na tabbata tana tare da kai.


kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.


Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.


Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.


Wani an yi masa baiwa da koyar da hikima ta wurin Ruhu, wani kuma da koyar da sani ta wurin wannan Ruhu.


To, da yake kun fifita a kowane abu, wato, a cikin bangaskiya, da magana, da sani, da matuƙar himma, da kuma ƙaunar da kuke yi mana, to, sai ku fifita a wannan aikin alheri ma.


Da wannan maƙasudi, a kullum muke yi muku addu'a, Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ya biya muku duk muradinku na yin nagarta, da aikin bangaskiya ta wurin ƙarfin ikonsa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ