10 Har wa yau kuma an ce, “Ya ku al'ummai, ku yi ta farin ciki tare da jama'arsa.”
10 Ya kuma ce, “Ku yi farin ciki, ya Al’ummai, tare da mutanensa.”
“Ya ku al'ummai, ku yabi jama'arsa, Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu, Zai ɗauki fansa a kan magabtansa, Zai tsarkake ƙasar jama'arsa.”
Ku raira waƙa ga Allah, ku mulkokin duniya, Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,
Ubangiji Sarki ne! Ki yi murna ke duniya! Ku yi murna, dukanku tsibiran da suke cikin tekuna!
Ku yi murna tare da Urushalima Ku yi farin ciki tare da ita, Dukanku da kuke ƙaunar birnin nan! Ku yi murna tare da ita yanzu, Dukanku da kuka yi makoki dominta!