Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 14:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Kada ka rushe aikin Allah saboda abinci kawai. Hakika dukan abu mai tsarki ne, amma mugun abu ne mutum yă zama sanadin tuntuɓe ga wani, ta wurin abin da yake ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 14:20
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma fa duk wanda ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni ya yi laifi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.”


Ga masu tsarkin rai duk al'amarinsu mai tsarki ne, marasa tsarkin rai kuwa marasa ba da gaskiya, ba wani al'amarinsu da yake mai tsarki, da zuciyarsu da lamirinsu duka marasa tsarki ne.


Sai ya sāke jin murya, ji na biyu, ta ce, “Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki.”


Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan'uwanku yin tuntuɓe.


Ba abin da yake shiga mutum ta baka ne yake ƙazanta shi ba, abin da yake fita ta baka yake ƙazanta mutum.”


Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Almasihu Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.


Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu.


Ga wani, bangaskiyarsa ta yardar masa cin kome, wanda bangaskiyarsa rarrauna ce kuwa, sai kayan gona kawai yake ci.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ