Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 14:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Don haka sai mu himmantu ga yin abubuwan da suke kawo salama, suke kuma kawo inganta juna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 14:19
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.


In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.


Ku rabu da mugunta, ku aikata alheri, Ku yi marmarin salama, ku yi ƙoƙarin samunta.


Kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai, don kyautata zamansa da kuma inganta shi.


Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, ku kuma zama a tsarkake, in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji.


Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku.


Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sane, dame za a daɗaɗa shi? Sai ku kasance da gishiri a zuciyarku, ku yi zaman lafiya da juna.”


“Albarka tā tabbata ga masu ƙulla zumunci, domin za a ce da su 'ya'yan Allah.


Ya rabu da mugunta, ya kama nagarta, Ya himmantu ga zaman lafiya, ya kuma dimance ta.


To, ƙaƙa abin yake ne, 'yan'uwa? Duk sa'ad da kuka taru, wani yakan yi waƙar yabon Allah, wani kuma koyar da Maganar Allah, wani bayani, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Sai dai a yi kome don ingantawa.


kamar dai yadda nake ƙoƙarin kyautata wa dukan mutane a cikin duk abin da nake yi, ba nema wa kaina amfani nake yi ba, sai dai in amfani mutane da yawa, don su sami ceto.


Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma, Ga jama'ar Allah su zauna tare kamar 'yan'uwa!


Don haka, sai ka guje wa mugayen sha'awace-sha'awacen ƙuruciya, ka dimanci aikin adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma salama, tare da waɗanda suke roƙon Ubangiji da zuciya tsarkakakkiya.


kada kuma su ɓata zarafinsu a wajen almara da yawan ƙididdigar asali marar iyaka, waɗanda sukan haddasa gardandami, a maimakon riƙon amanar al'amuran Allah da bangaskiya.


Ashe, tun dā tsammani kuke yi muna kawo hanzarinmu a gare ku ne? A'a, a gaban Allah muke magana, muna na Almasihu, wannan kuwa duk domin inganta ku ne, ya ku ƙaunatattu.


In kuwa shi, ko ita, marar ba da gaskiya ɗin yana son rabuwa, to, sai su rabu. A wannan hali, ɗan'uwa ko 'yar'uwa mai bi, ba tilas a kansu, domin Allah ya kira mu ga zaman lafiya.


To, yanzu a game da abubuwan da aka yanka wa gumaka, mun sani dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kumbura mutum, ƙauna kuwa takan inganta shi.


“Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Dukan abubuwa halal ne,” amma ba dukan abubuwa ne suke ingantawa ba.


Wanda kuwa yake yin annabci, mutane yake yi wa magana domin yă inganta su, ya ƙarfafa su, yă ta'azantar da su.


Duk wanda yake magana da wani harshe, kansa yake ingantawa. Mai yin annabci kuwa, ikkilisiya yake ingantawa.


To, ina so dukanku ku yi magana da waɗansu harsuna dabam, amma na fi so ku yi annabci. Wanda yake yin annabci, ya fi mai magana da waɗansu harsuna, sai ko in wani ya yi masa fassara, domin a inganta ikkilisiya.


domin tsarkaka su samu, su iya aikin hidimar Ikkilisiya, domin a inganta jikin Almasihu,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ