Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 14:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A game da wanda bangaskiya tasa rarrauna ce kuwa, ku karɓe shi hannu biyu biyu, amma ba a game da sukan ra'ayinsa ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 14:1
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

To, mu da muke ƙarfafa, ya kamata mu ɗauki nauyin raunana, kada mu yi sonkai.


Ga raunana, sai na zama kamar rarrauna domin in rinjayi raunana. Na zama kowane irin abu ga ko waɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu.


Saboda haka ku karɓi juna da hannu biyu biyu, kamar yadda Almasihu ya karɓe ku hannu biyu biyu, domin a ɗaukaka Allah.


Ya kyautu kada ma ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko kuwa ka yi kowane irin abu, wanda zai sa ɗan'uwanku yin tuntuɓe.


Kowa ya zo gare ku, bai kuwa zo da wannan koyarwa ba, kada ku karɓe shi a gidanku, ko maraba ma kada ku yi masa.


Bangaskiyarsa kuwa ba ta raunana ba, bai dubi gajiyawar jikinsa ba, don yana da shekara wajen ɗari a lokacin, ko kuma cewa Saratu ta wuce haihuwa.


Da dai wani ya sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara ya yi laifi, zai fiye masa a rataya wani dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi a cikin teku.


Nan da nan Yesu ya miƙa hannu ya kamo shi, ya ce masa, “Ya kai mai ƙarancin bangaskiya, don me ka yi shakka?”


Kyauron da ya tanƙwasa ba zai kakkarye shi ba, Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, Har ya sa gaskiya ta ci nasara.


Zai lallaɓi marasa ƙarfi, Ya nuna alheri ga tafkakku. Zai kawo madawwamiyar gaskiya ga duka.


Zai lura da garkensa kamar yadda makiyayi suke yi, Zai tattara 'yan raguna wuri ɗaya, Zai ɗauke su ya rungume su, A hankali zai bi da iyayensu.


Ka koya wa mutane da yawa, Ka kuma ƙarfafa hannuwan marasa ƙarfi.


“Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.


Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji.


Don haka sai ku karɓe shi da matuƙar farin ciki saboda Ubangiji, ku kuma girmama irin waɗannan mutane,


Lalle hakika, ina gaya muku, wanda ya yi na'am da duk wanda na aiko, ya yi na'am da ni ke nan. Wanda ya yi na'am da ni kuwa, to, ya yi na'am da wanda ya aiko ni.”


“Ku dai lura, kada ku raina ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara. Ina gaya muku, mala'ikunsu a Sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin Sama.


Gama ga shi, zan sa wani makiyayi a ƙasan nan, wanda ba zai kula da masu lalacewa ba, ko waɗanda suka warwatse, ko ya warkar da gurgu, ko ya ciyar da waɗanda suka ragu, amma zai ci naman masu ƙiba, ya farfashe kofatonsu.


tun da yake ba zuciya tasa ya shiga ba, cikinsa ne, ta haka kuma zai fita?” Ta haka Yesu ya halatta kowane irin abinci.


Mutanen garin kuwa sun yi mana alheri matuƙar alheri, don sun hura wuta sun karɓe mu, mu duka, saboda ana ruwa, ga kuma sanyi.


Domin in an sulhunta duniya ga Allah, saboda yar da su da aka yi, to, in an karɓe su fa, ba sai rai daga matattu ba?


Ga wani, bangaskiyarsa ta yardar masa cin kome, wanda bangaskiyarsa rarrauna ce kuwa, sai kayan gona kawai yake ci.


To, kada fa mai cin kome ɗin nan yă raina wanda ya ƙi ci, kada kuma wanda ya ƙi cin nan, yă ga laifin mai ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi hannu biyu biyu.


Muna kuma yi muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku tsawata wa malalata, ku ƙarfafa masu rarraunar zuciya, ku taimaki marasa tsayayyiyar zuciya, ku yi haƙuri da kowa da kowa.


Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ