10 Ƙauna ba ta cutar maƙwabci saboda haka ƙauna cika Shari'a ce.
10 Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.
Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari'a ke nan.
Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”
Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna.
Don duk Shari'a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
Idan lalle kun cika muhimmin umarni yadda Nassi ya ce, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” to, madalla.