Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 13:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Bari kowa yă yi biyayya ga mahukunta. Gama ba wani iko sai da yardar Allah. Mahukuntan da suke nan kuwa naɗin Allah ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 13:1
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka riƙa tuna musu su yi wa mahukunta da shugabanni ladabi, suna yi musu biyayya, suna kuma zaune da shirinsu na yin kowane irin kyakkyawan aiki.


Yana da ikon sāke lokatai, Yakan tuɓe sarakuna, ya kuma naɗa waɗansu. Yana ba masu hikima hikima, masu ilimi kuwa fahimi,


Yesu ya amsa masa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina in ba an ba ka daga Sama ba, saboda haka wanda ya bāshe ni gare ka ya fi ka zunubi.”


Haka kuma masu mafarke-mafarken nan, sukan ƙazantar da jikinsu, su ƙi bin mulki, su kuma yi wa masu ɗaukaka baƙar magana.


Sau ɗaya Allah ya faɗa, Sau biyu na ji, cewa Allah yake da iko.


Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura, Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki. Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki, Ya ɗora su a wurare masu maƙami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu ya kafa duniya.


Da wani suna a rubuce a jikin rigarsa, har daidai cinyarsa, wato Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.


da kuma Yesu Almasihu Amintaccen Mashaidi, na farko a cikin masu tashi daga matattu, mai mulkin sarakunan duniya. Ɗaukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wanda yake ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubanmu ta wurin jininsa,


Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.”


Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”


Kada ka kai mu wurin jaraba, Amma ka cece mu daga Mugun.’


Duk wanda ya yi izgili, ya ƙi yin biyayya da firist wanda yake a can, yana yi wa Ubangiji Allahnku hidima, ko kuma ya ƙi yi wa alƙalin biyayya, to, lalle sai a kashe wannan mutum. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikin Isra'ilawa.


Ɗana, ka yi tsoron Ubangiji, ka kuma ji tsoron sarki, kada ka yi harkar kome da mutanen da suka tayar musu.


Wannan shi ne hukuncin da tsarkaka, Masu tsaro suka shawarta, Suka yanke domin masu rai su sani Maɗaukaki yake sarautar 'yan adam, Yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama, Yakan sa talaka ya zama sarki.’


Waɗanda suka ya na'am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku.


Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.


Saboda haka duk wanda ya yi wa mahukunta tsayayya, ya yi wa umarnin Allah ke nan, masu yin tsayayyar nan kuwa za a yi musu hukunci.


da sarakuna da kuma duk waɗanda suke a manyan maƙamai, don mu zauna lafiya, rai a kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ