Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 12:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Da yake muna da baiwa iri iri, gwargwadon alherin da aka yi mana, to, sai mu yi amfani da su. In ta annabci ce, sai mu yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarmu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 12:6
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da ma a ce kowa kamar ni yake mana! Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa, wani iri kaza, wani kuma iri kaza.


Albarkacin alherin da aka yi mini ina yi wa kowannenku gargaɗi kada ya ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, sai dai ya san kansa, gwargwadon bangaskiyar da Allah ya ba shi.


Domin ina ɗokin ganinku, in ni'imta ku da wata baiwa ta ruhu, domin ku ƙarfafa.


Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.


Ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa,


Ku nace wa ƙauna, ku kuma himmantu ga neman bayebaye na ruhu, tun ba ma na yin annabci ba.


Domin mutum yana da niyyar bayarwa, bayarwarsa za ta zama abar karɓa ce, bisa ga yawan abin da yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.


Masu yin annabci kuma, sai dai biyu ko uku su yi magana, saura kuwa su auna maganar.


Yahuza da Sila kuma, da yake su annabawa ne, suka gargaɗi 'yan'uwa da maganganu masu yawa, suka kuma ƙarfafa su.


“ ‘Allah ya ce, A zamanin karshe zai zamanto zan zubo wa dukan 'yan adam Ruhuna. 'Ya'yanku mata da maza za su yi annabci, Wahayi zai zo wa samarinku, Dattawanku kuma za su yi mafarkai.


Saboda haka ɗaukacin waɗanda suka kammala a cikinmu, sai su bi wannan ra'ayi. In kuwa a game da wani abu ra'ayinku ya sha bambam, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma.


wanda a zamanin dā ba a sanar da 'yan adam ba, kamar yadda a yanzu aka bayyana wa manzanninsa tsarkaka da annabawa, ta wurin Ruhu,


To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu.


Shi ya sa hikimar Allah ta ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni, su kashe waɗansu,’


Saboda haka nake aiko muku da annabawa, da masu hikima, da masanan Attaura, za ku kashe waɗansunsu, ku gicciye waɗansu, ku kuma yi wa waɗansu bulala a majami'unku, kuna binsu gari gari kuna gwada musu azaba.


In kuwa kowa yana yin annabci, wani kuma marar ba da gaskiya ko jahili ya shigo, sai maganar kowa ta ratsa shi, ya kamu a ransa ta maganar kowa,


Shi kuwa yana da 'ya'ya huɗu 'yan mata, masu yin annabci.


To, wane ne Afolos? wane ne Bulus kuma? Ashe, ba bayi ne kawai ba, waɗanda kuka ba da gaskiya ta wurinsu, ko wannensu kuwa gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi?


Amma ga shi, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowaccensu yadda ya nufa.


Da farko dai, lalle ne ku fahimci wannan cewa, ba wani annabci a Littattafai da za a iya fassarawa ta ra'ayin mutum.


Sai mai talanti biyun nan kuma ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, kā ba ni talanti biyu, ga shi kuma, na ci ribar biyu.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ