21 Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.
21 Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.
Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.
Ya fi kyau ka zama mai haƙuri da ka zama mai ƙarfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.
Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.”
Bari kowa yă yi biyayya ga mahukunta. Gama ba wani iko sai da yardar Allah. Mahukuntan da suke nan kuwa naɗin Allah ne.