Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku.
Don haka, sai ka guje wa mugayen sha'awace-sha'awacen ƙuruciya, ka dimanci aikin adalci, da bangaskiya, da ƙauna, da kuma salama, tare da waɗanda suke roƙon Ubangiji da zuciya tsarkakakkiya.
In kuwa shi, ko ita, marar ba da gaskiya ɗin yana son rabuwa, to, sai su rabu. A wannan hali, ɗan'uwa ko 'yar'uwa mai bi, ba tilas a kansu, domin Allah ya kira mu ga zaman lafiya.