Na rubuto muku haka ne, don kada in na zo, waɗanda ya kamata su faranta mini rai, ya zamana sun sa ni baƙin ciki. Domin na amince da ku duka, cewa farin cikina naku ne ku duka.
Sa'ad da uku daga cikin abokan Ayuba, wato Elifaz daga birnin Teman, da Bildad daga ƙasar Shuwa, da Zofar daga ƙasar Na'ama, suka ji labarin irin yawan wahalar da Ayuba yake sha, sai suka kama hanya suka tafi su ziyarce shi, su ta'azantar da shi.