14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la'ance su.
14 Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta.
Kada ku rama mugunta da mugunta, ko zagi da zagi, a maimakon haka, sai ku sa albarka. Domin a kan haka ne musamman aka kira ku, ku kuma gaji albarka.
Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu'a,
Ku lura fa, kada kowa ya rama mugunta da mugunta. Sai dai kullum ku nace yi wa juna aiki nagari, da kuma dukkan mutane.
Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.
Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakanta ku kuma, ku yi musu addu'a.
Da baki ɗaya ake yabo, ake kuma zagi. 'Yan'uwana, ai, wannan bai kamata ba!
Sai Yesu ya ce, “Ya Uba, ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa, suna kuri'a a kansu.
Sa'an nan ya durƙusa, ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Ya Ubangiji, kada ka ɗora musu wannan zunubi.” Da faɗar haka sai ya yi barci.