Waɗancan sun zama firistoci, ba tare da an yi musu rantsuwa ba, amma wannan kam, sai da aka yi masa rantsuwa, da Allah ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, Ba kuwa zai ta da maganarsa ba cewa, ‘Kai firist ne har abada.’ ”
Ku dubi kiranku da aka yi, ya ku 'yan'uwa, a cikinku, ai, ba a kira masu hikima irin ta duniya da yawa ba, masu iko kuma ba su da yawa, haka ma masu asali ma ba yawa.
a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka,
Da wannan maƙasudi, a kullum muke yi muku addu'a, Allahnmu yă sa ku cancanci kiransa, ya biya muku duk muradinku na yin nagarta, da aikin bangaskiya ta wurin ƙarfin ikonsa,
wanda ya cece mu, ya kuma kira mu da kira mai tsarki, ba don wani aikin lada da muka yi ba, sai dai domin nufinsa, da kuma alherinsa, da aka yi mana baiwa tun fil'azal, a cikin Almasihu Yesu,
Saboda haka, ya ku 'yan'uwa tsarkaka, ku da kuke da rabo a kiran nan basamaniya, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa,
Saboda haka, ya ku 'yan'uwa, ku ƙara ba da himma ku tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Domin in kun bi waɗannan halaye, ba za ku fādi ba har abada.