Ba za a gafarta zunuban Isra'ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.
Ubangiji ya ce, “Amma ni, wannan shi ne alkawarina da su, Ruhuna da yake tare da ku, da kalmomina da na sa a bakunanku, ba za su rabu da bakunanku ba, ko daga bakunan 'ya'yanku, ko na jikokinku, tun daga wannan lokaci har abada.”
“Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu,”
Ni Ubangiji na ce sa'ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra'ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu.
“Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai! Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.