Ubangiji ya ce, “Ga shi, waɗanda ba a shara'anta su ga shan ƙoƙon hukunci ba, za su sha shi, to, kai za ka kuɓuta? Ba za ka kuɓuta ba, amma lalle za ka sha shi!
Gama ga shi, na fara sa masifa ta yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana. To, kuna tsammani ba za a hukunta ku ba? Sai an hukunta ku, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’
Sai dai ina so in tuna muku, ko da yake kun riga kun san kome sosai, cewa Ubangiji ya ceci jama'a daga ƙasar Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.
Amma in an sassare waɗansu rassan zaitun na gida, kai kuma da kake zaitun na jeji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni'imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,
Hakika haka ne, amma saboda rashin bangaskiyarsu ne aka sare su, kai kuwa saboda bangaskiyarka ne kake kafe. Kada fa ka nuna alfarma, sai dai ka ji tsoron Allah.
Dubi fa alherin Allah da kuma tsananinsa, wato, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, alherinsa kuwa a gare ka, muddin ka ɗore a cikin alherin. In ba haka ba, kai ma sai a datse ka.