Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 10:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Amma me Nassi ya ce? “Maganar, ai, tana kusa da kai, tana ma a bakinka, da kuma a cikin zuciyarka.” Ita ce maganar bangaskiya da muke wa'azi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 10:8
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma umarnin yana kurkusa da ku, yana cikin bakinku da zuciyarku don ku kiyaye shi.


In kana tuna wa 'yan'uwa wadannan abubuwa, za ka zama amintaccen bawan Almasihu Yesu, wanda aka goya da maganar bangaskiya, da kuma sahihiyar koyarwar nan wadda ka bi har ya zuwa yau.


Maganar Ubangiji kuwa dawwamammiya ce,” Ita ce maganar bishara da aka yi muku.


Abu ɗaya kaɗai zan tambaye ku. Kun sami Ruhu saboda bin Shari'a ne, ko kuwa saboda gaskatawa ga maganar da kuka ji?


Wato, shi da yake yi muku baiwar Ruhu, yake kuma yin mu'ujizai a cikinku, saboda kuna bin Shari'a ne yake yin haka, ko kuwa saboda gaskatawa da maganar da kuka ji?


Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta Maganar Almasihu yake.


Shi ne duk annabawa suka yi wa shaida, cewa albarkacin sunansa duk mai gaskatawa da shi zai sami gafarar zunubai.”


Gama sāke haifuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dawwamammiya.


Su kuwa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”


Salama, salama,” in ji Ubangiji, “Ga wanda yake nesa da wanda yake kusa. Zan warkar da su.


domin ya miƙa ta ga Allah, tsarkakakkiya bayan da ya wanke ta da ruwa ta wurin Kalma,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ