Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 10:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji. “Muryarsu ta gama duniya duka, Maganarsu kuma ta kai har bangon duniya.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Amma ina tambaya, “Ba su ji ba ne? Tabbatacce sun ji. “Muryarsu ta tafi ko’ina a cikin duniya, kalmominsu kuma har iyakar duniya.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 10:18
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duk da haka muryarsu ta game duniya duka, Saƙonsu ya kai ko'ina a duniya. Allah ya kafa wa rana alfarwa a sararin sama,


Da farko dai ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko'ina a duniya.


Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko'ina a duniya domin shaida ga dukkan al'ummai. Sa'an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”


Domin daga gare ku ne aka baza Maganar Ubangiji, ba ma a ƙasar Makidoniya da ta Akaya kaɗai ba, har ma a ko'ina bangaskiyarku ga Allah ta shahara, har ma ya zamana, ba sai lalle mun faɗa ba.


Sai dai fa ku nace wa bangaskiya, zaunannu, kafaffu, ba tare da wata ƙaura daga begen nan na bishara wadda kuka ji ba, wadda aka yi wa dukkan talikan da suke a duniya, wadda kuma ni Bulus na zama mai hidimarta.


wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.


Sai ya ce musu, “Ku tafi ko'ina a duniya, ku yi wa dukkan 'yan adam bishara.


Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al'ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki,


Hakika, ina gaya muku, duk inda za a yi bisharar nan a duniya duka, abin da matar nan ta yi za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”


“Ya Ubangiji, ƙarfina da kagarata, Mafakata a ranar wahala, A gare ka al'ummai za su zo, Daga ƙurewar duniya, su ce, ‘Kakanninmu ba su gāji kome ba, sai ƙarya, Da abubuwan banza marasa amfani.’


Har wa yau dai, sai Iblis ya kai shi kan wani dutse mai tsawo ƙwarai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.


Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki, Ya ceci jama'arsa, Dukan duniya kuwa ta gani.


Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”


Ya cika alkawarinsa wanda ya yi wa jama'ar Isra'ila, Da tabbatacciyar ƙauna da aminci. Dukan mutane ko'ina sun ga nasarar Allahnmu!


Dukan al'ummai za su tuna da Ubangiji, Za su zo gare shi daga ko'ina a duniya, Dukan kabilai za su yi masa sujada.


Daga manisantan wurare na duniya za mu ji waƙoƙin yabon Isra'ila, al'umma adala. Amma ba ni da sauran sa zuciya! Lalacewa nake yi! Maciya amana suna ta cin amana, cin amanarsu sai gaba gaba yake yi.


Na rantse da Ubangiji Allahnka mai rai, ba al'umma ko mulki da shugabana sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka nan, sai ya sa mulkin ko al'ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba.


ta wurin ikon mu'ujizai, da abubuwan al'ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko'ina.


Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.


Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa'azi ko'ina, Ubangiji yana taimakonsu, yana kuma tabbatar da maganarsu ta mu'ujizan nan da suke biye da maganar.]


Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa'azi, sa'an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa'an nan kuma na yi wa al'ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.


Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ