Yanzu fa ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan kafa ƙaƙƙarfan harsashin gini a Sihiyona. A kansa zan sa ƙaƙƙarfan dutsen kusurwa. A kansa an rubuta wannan magana, ‘Amincin da yake kafaffe mai haƙuri ne kuma.’
Domin a tabbace yake a Nassi cewa, “Ga shi, na sa mafificin dutsen a gini a Sihiyona, zaɓaɓɓe, ɗaukakakke, Duk mai gaskatawa da shi kuwa, ba zai kunyata ba.”
Sarakuna za su zama kamar iyaye a gare ku, Sarauniyoyi za su yi renonku kamar uwaye. Za su rusuna har ƙasa su ba ku girma, Da tawali'u za su nuna muku bangirma. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji, Dukan mai jiran taimakon Ubangiji, ransa ba zai ɓaci ba.”