Romawa 10:10 - Littafi Mai Tsarki10 Domin da zuci mutum yake gaskatawa yă sami adalcin Allah, da baki yake shaidawa yă sami ceto. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
da yake mun sani mutum ba ya samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, sai dai ta wurin gaskatawa ga Yesu Almasihu kaɗai, mu ma mun gaskata da Almasihu Yesu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya ga Almasihu, ba ta wurin bin Shari'a ba, don ba ɗan adam ɗin da zai sami kuɓuta ga Allah ta hanyar bin Shari'a.