Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 1:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Da farko dai ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko'ina a duniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a ko’ina a duniya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 1:8
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma ku kam, ai, kowa ya san biyayyarku, shi ya sa nake farin ciki da ku. Sai dai ina so ku gwanance da abin da yake nagari, amma ya zama ba ruwanku da mugunta.


Kullum nakan gode wa Allah dominku, saboda alherin Allah da aka yi muku baiwa ta hanyar Almasihu Yesu,


Amma godiya tā tabbata ga Allah, ko da yake dā can ku bayin zunubi ne, a yanzu kam kuna biyayya da zuciya ɗaya ga irin koyarwar nan da aka yi muku.


Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!


Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu,


To, a koyaushe, sai mu yi ta yabon Allah ta wurinsa, sadakar da muke miƙawa ke nan, wato mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa.


A kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu, duk sa'ad da muke yi muku addu'a,


Ina gode Allahna duk sa'ad da nake tunawa da ku,


Saboda haka da yake na ji labarin bangaskiyarku ga Ubangiji Yesu, da kuma ƙaunarku ga dukan tsarkaka,


kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin ɗaukakar Allah ne, da yabonsa.


Kullum ku riƙa gode wa Allah Uba da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a kan ko mene ne.


Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko'ina a duniya domin shaida ga dukkan al'ummai. Sa'an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”


Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a cikin Ikkilisiya ta wurin Almasihu Yesu, har ya zuwa dukkan zamanai har abada abadin. Amin.


Sai ɗaya daga cikinsu, mai suna Agabas, ya miƙe tsaye, ya yi faɗi da ikon Ruhu, cewa za a yi wata babbar yunwa, a duniya duka, an yi ta kuwa a zamanin Kalaudiyas.


A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da suke ƙarƙashin mulkinsa.


Amma muna so mu ji daga bakinka abin da yake ra'ayinka, don in dai ta ɗariƙar nan ne, mun sani ko'ina ana kushenta.”


Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji. “Muryarsu ta gama duniya duka, Maganarsu kuma ta kai har bangon duniya.”


Amma godiya ta tabbata ga Allah, shi da kullum yake yi mana jagaba mu ci nasara, albarkacin Almasihu, ta wurinmu kuma yake baza ƙanshin nan, na sanin Almasihu a ko'ina.


ban fāsa gode wa Allah saboda ku ba, duk sa'ad da nake yi muku addu'a,


A kullum muna gode wa Allah saboda ku duka, koyaushe muna ambatonku a cikin addu'armu,


Saboda wannan ne kuma muke gode wa Allah ba fasawa, domin sa'ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, Maganar Allah, wadda take aiki a cikin zuciyarku, ku masu ba da gasikya.


Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, 'yan'uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.


Ina gode wa Allah, wanda nake bauta wa da lamiri mai tsabta, kamar yadda kakannina suka yi, duk sa'ad da nake tunawa da kai a cikin addu'ata ba fāsawa.


A kullum ina gode wa Allahna duk sa'ad da nake yi maka addu'a,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ