Ubangiji ya ce, “Mutanena wawaye ne, Ba su san ni ba, Yara ne dakikai, Ba su da ganewa. Suna gwanance da aikin mugunta, Amma ba su san yadda za su yi nagarta ba.”
Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.