Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Romawa 1:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Saboda haka Allah ya sallama su ga rashin tsarkaka ta mugayen sha'awace-sha'awacensu, har su wulakanta jikinsu a junansu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Romawa 1:24
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka Allah ya juya musu baya, ya sallame su ga bautar taurari, yadda yake a rubuce a littafin annabawa cewa, “ ‘Ya ku jama'ar Isra'ila, Ni ne kuka yanka wa dabbobi, kuka miƙa wa hadaya, Har shekara arba'in a cikin jeji?


Shi ne a zamanin dā, ya bar dukan al'ummai su yi yadda suka ga dama.


Ƙyale su kawai, makafin jagora ne. In kuwa makaho ya yi wa makaho jagora, ai, duk biyu sai su faɗa a rami.”


Kada ya yi luɗu, gama Allah yana ƙin wannan.


kowannenku kuma ya san yadda zai auro matarsa da tsarki da mutunci,


Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubin da mutum yake yi bai shafi jikinsa ba, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne.


“Abinci don ciki aka yi shi, ciki kuma don abinci” – Allah kuma zai hallaka duka biyu, wannan da wancan. Jiki kam, ba don fasikanci yake ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.


Saboda haka, kada ku yarda zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa har da za ku biye wa muguwar sha'awarsa.


Dukkanmu dā mun zauna a cikinsu, muna biye wa sha'awoyin halin mutuntaka, muna aikata abin da jiki da zuciya suke buri, har ma ga ɗabi'a wajibi ne fushin Allah ya bayyana a kanmu, kamar sauran 'yan adam.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ