Ɗaukaka tă tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa'azin Yesu Almasihu, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil'azal.
Na rubuto muku wasiƙar nan a taƙaice ta hannun Sila, ɗan'uwa mai aminci, a yadda na ɗauke shi, domin in yi muku gargaɗi, in kuma sanar da ku, cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske, ku tsaya a gare shi da ƙarfi.
Bayan kun sha wuya kuma ta ɗan lokaci kaɗan, Allah mai alheri duka, wanda ya kira ku ga samun madawwamiyar ɗaukakarsa a cikin Almasihu, shi kansa zai kammala ku, ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku.
Sai suka tashi da sassafe suka tafi jejin Tekowa. Sa'ad da suka fita sai Yehoshafat ya tsaya, ya ce, “Ku saurara gare ni, ku mutanen Yahuza da mazaunan Urushalima. Ku gaskata da Ubangiji Allahnku, za ku kahu. Ku gaskata annabawansa, za ku ci nasara.”
Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.
Bayan waɗannan al'amura Bulus ya ƙudura a ransa, cewa in ya zazzaga ƙasar Makidoniya da ta Akaya, za shi Urushalima, ya kuma ce, “Bayan na je can, lalle ne kuma in je in ga birnin Roma.”
Kada baƙuwar koyarwa iri iri ta bauɗar da ku, ai, abu ne mai kyau alherin Allah ya zamana shi yake ƙarfafa zuciya, ba abinci iri iri ba, waɗanda ba su amfani ga masu dogara da su.
Don in wani ya zo yana wa'azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa'azi, ko kuma in kun sami wani ruhu dabam da Ruhun da kuka samu, ko wata bishara dabam da wadda kuka yi na'am da ita, ashe, har kuna saurin yin na'am da irinsu ke nan!