Tafi, ka tattara dattawan Isra'ila, ka faɗa musu, ‘Ubangiji Allah na kakanninku ya bayyana gare ni, wato na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, ya ce, sosai ya ziyarce ku, ya kuma ga abin da ake yi muku a Masar.
Isra'ilawa suka ga gawurtaccen aikin da Ubangiji ya yi gāba da Masarawa. Isra'ilawa kuwa suka ji tsoron Ubangiji, suka gaskata Ubangiji da bawansa Musa.
a ran nan na rantse musu, cewa zan fito da su daga ƙasar Masar, zuwa wata ƙasa wadda na samo musu, ƙasar da take da yalwar albarka, wato ƙasa mai albarka duka.