Nehemiya 9:4 - Littafi Mai Tsarki4 Sai Yeshuwa, da Bani, da Kadmiyel, da Shebaniya, da Bunni, da Sherebiya, da Bani, da Kenani suka tsaya a kan dakalin Lawiyawa, suka ta da murya da ƙarfi ga Ubangiji Allahnsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 A kan dakalin kuwa akwai Lawiyawa, wato, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani da Kenani tsaye, waɗanda suka kira da babbar murya ga Ubangiji Allahnsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗannan Lawiyawa kuma, wato Yeshuwa, da Kadmiyel, da Bani, da Hashabnaiya, da Sherebiya, da Hodiya, da Shebaniya, da Fetahiya su ne suka yi kiran sujada, suka ce, “Ku miƙe tsaye, ku yabi Ubangiji Allahnku, Ku yabe shi har abada abadin. Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka, ya Ubangijii, Ko da yake ba yabon da ɗan adam zai yi har ya isa.”
Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.