Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 9:37 - Littafi Mai Tsarki

37 Amfanin ƙasa duk yana tafiya ga sarakunan Da ka ɗora su a kanmu saboda mun yi zunubi. Suna yi mana yadda suka ga dama, mu da dabbobinmu, Muna cikin baƙin ciki.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

37 Saboda zunubanmu, yalwar girbin da muke samu yana tafiya wurin sarakunan da ka sa a kanmu. Suna mulki bisa jikunanmu, da bisa garkenmu yadda suka ga dama. Muna cikin baƙin ciki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 9:37
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mutanen da ba ku sani ba, su za su ci amfanin gonakinku da dukan amfanin wahalarku. Za a zalunce ku, a murƙushe ku kullum.


domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku.


Muna kuma sanar da ku, cewa ba daidai ba ne ku karɓi haraji, da kuɗin shiga da fita, daga wurin firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da matsaran ƙofa, da masu lura da Haikali, da ma'aikatan wannan Haikali na Allah.


Suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne, ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya kuma za ka ce za a 'yanta mu?”


Na ce musu, “Da iyakacin ƙoƙarinmu mun fanshi 'yan'uwanmu Yahudawa waɗanda aka sayar wa al'ummai, amma ga shi, kuna tilasta wa 'yan'uwanku su sayar da kansu ga 'yan'uwansu.” Sai suka yi tsit, suka rasa abin da za su ce.


Ina umartarku ku biya wa dattawan Yahuza kuɗin sāke ginin Haikalin nan na Allah, a biya mutanen nan cikakken kuɗin aiki daga baitulmalin sarki, wanda yake a lardin Yammacin Kogi, ba tare da ɓata lokaci ba.


Sarki ya sani fa, idan an sāke gina birnin, aka kuma gama garun, ba za su biya haraji ko kuɗin shiga da fita na kaya ko kuɗin fito ba, baitulmalin sarki za ta rasa kuɗi ke nan.


Za ta ci shanunku da amfanin ƙasarku har ku hallaka. Ba za ta bar muku hatsi ko ruwan inabi, ko mai, ko 'ya'yan shanunku, ko na tumaki da na awakinku ba, har ta lalatar da ku.


Za ku dasa gonakin inabi, ku nome su, amma ba za ku sha ruwan inabin, ko ku tsinke 'ya'yan inabin ba, gama tsutsa za ta cinye shi.


Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku.


Masu binmu a ƙyeyarmu suke, suna korarmu da zafi, Mun gaji, ba a yarda mu huta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ