Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 9:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Saboda haka ka bar abokan gābansu su ci su, mallake su. A wahalarsu sun yi kira gare ka domin taimako, Ka kuwa amsa musu daga Sama. Ta wurin jinƙanka mai yawa ka aiko musu da shugabanni, Waɗanda suka kuɓutar da su daga maƙiyansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Saboda haka ka miƙa su ga abokan gābansu waɗanda suka yi musu danniya. Amma sa’ad da ake danniyarsu sai suka yi kuka gare ka. Daga sama ka ji su, cikin jinƙanka mai girma kuwa ka ba su mai ceto, wanda ya fisshe su daga hannun abokan gābansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 9:27
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji kuwa bai ce zai shafe sunan Isra'ila daga duniya ba, saboda haka ya cece su ta hannun Yerobowam na biyu.


Saboda haka Ubangiji ya ba jama'ar Isra'ila maceci, suka kuwa kuɓuta daga ƙangin Suriyawa, suka zauna a gidajensu lafiya kamar dā.


Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa.


Sa'ad da Ubangiji ya naɗa musu mahukunci, yakan taimake shi, ya kuwa cece su daga abokan gāba dukan kwanakin mahukuncin. Gama Ubangiji ya ji ƙansu saboda nishinsu, da zaluncin da ake yi musu.


Isra'ilawa za su hau Dutsen Sihiyona, su cece shi, Za su mallaki dutsen Isuwa, Ubangiji ne Sarki.


Amma ba ka rabu da su a hamada ba, Saboda jinƙanka mai girma ne. Ba ka kuwa kawar da girgije da wuta ba, Waɗanda suke nuna musu hanya dare da rana.


Zan yi gāba da ku in sa maƙiyanku su ɗibge ku, waɗanda suke ƙinku za su mallake ku. Za ku yi ta gudu ba mai korarku.


Ubangiji kuwa ya ƙi dukan zuriyar Isra'ila, ya wahalshe su, ya kuma bashe su a hannun mugayen abokan gāba, ta haka ya kawar da su daga gabansa.


Amma su yi tsoron Ubangiji Allahnsu, shi kuwa zai cece su daga hannun dukan abokan gābansu.


Ya 'yantar da mu daga abokan gābanmu, Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ