Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 9:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Saboda haka zuriyarsu suka shiga, suka mallaki ƙasar Kan'ana. Ka rinjayi mutanen da suke zama a can. Ka ba jama'arka iko su yi yadda suke so Da mutane, da sarakunan ƙasar Kan'ana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 ’Ya’yansu maza suka shiga suka kuma mallaki ƙasar. A gabansu ka rinjayi Kan’aniyawan da suke zama a cikin ƙasar; ka ba da Kan’aniyawa a gare su, tare da sarakunansu da kuma mutanen ƙasar, su yi da su yadda suke so.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 9:24
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Haka kuwa Ubangiji ya ba Isra'ilawa dukan ƙasar da ya rantse zai ba kakanninsu. Suka ci ƙasar, suka zauna a ciki.


Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.


Haka nan kuwa Joshuwa ya ci dukan ƙasar yadda Ubangiji ya faɗa wa Musa. Ya kuwa ba da ƙasar gādo ga Isra'ilawa kabila kabila. Ƙasar kuwa ta shaƙata da yaƙi.


su kuɓuce wa tarkon Iblis, su bi nufin Allah, bayan da Iblis ya tsare su.


Ya ce, “Ubangiji Allahnku yana tare da ku, ya ba ku zaman lafiya a kowane sashi. Gama ya ba da mazaunan ƙasar a hannuna, an murƙushe ƙasar a gaban Ubangiji da jama'arsa.


Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alheri da ya yi wa gidan Isra'ila.


Amma 'yan ƙanananku, waɗanda kuka ce za su zama ganima, su ne zan kai su cikin ƙasar, za su san ƙasar da kuka raina.


A wannan rana Allah ya fatattaki Yabin Sarkin Kan'ana, a gaban Isra'ilawa.


Haka nan kuwa Joshuwa ya cinye dukan ƙasar tuddai, da Negeb, da filayen kwaruruka, da gangare, da sarakunansu duka, ba wanda ya ragu, amma ya hallaka su duka kamar yadda Ubangiji, Allah na Isra'ila ya umarta.


da Sarkin Tirza. Sarakuna talatin da ɗaya ke nan.


Yahudawa kuwa suka kashe dukan maƙiyansu da takobi. Suka hallaka maƙiyansu yadda suke so.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ