Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 9:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Ka ba su abinci daga sama sa'ad da suka ji yunwa, Ruwa kuma daga dutse sa'ad da suka ji ƙishi, Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka yi alkawari za ka ba su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Cikin yunwansu ka ba su burodi daga sama, cikin ƙishirwansu kuma ka fitar musu ruwa daga dutse. Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka rantse ta wurin ɗaga hannu cewa za ka ba su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 9:15
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duba, na sa ƙasar a gabanku, sai ku shiga ku mallake ta, ƙasa wadda na rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, cewa zan ba su, su da zuriyarsu a bayansu.’ ”


Zan tsaya a dutsen Horeb can a gabanka. Za ka bugi dutsen, ruwa kuwa zai fito domin jama'a su sha.” Musa kuma ya yi haka nan a gaban dattawan Isra'ila.


Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Ga shi, zan sauko muku da abinci daga sama. A kowace rana jama'a za su fita su tattara abin da zai ishe su a yini, da haka zan gwada su, ko za su kiyaye maganata, ko babu.


Na kuma rantse musu a cikin jeji, cewa ba zan kai su ƙasar da na ba su ba, ƙasar da take cike da yalwar albarka, wato ƙasar da take mafi albarka duka,


Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa, Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai, Masu bulbulo da ruwa.


Ya koya muku tawali'u, ya bar ku da yunwa, ya ciyar da ku da manna wadda ba ku sani ba, kakanninku kuma ba su sani ba, domin ya sa ku sani, ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, amma mutum yana rayuwa da kowane irin abin da yake fitowa daga wurin Ubangiji.


Ta wurin alherinka ka faɗa musu abin da ya kamata su yi, Ka ciyar da su da manna, ka ba su ruwa su sha.


Ga ƙasar a gabanku wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku, sai ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allah na kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro ko ku firgita.’


ba wanda zai shiga ƙasar da na rantse ta zama wurin zamanku, sai Kalibu, ɗan Yefunne, da Joshuwa ɗan Nun.


Amma Abram ya ce wa Sarkin Saduma, “Na riga na rantse wa Ubangiji Allah Maɗaukaki, wanda ya yi sama da ƙasa,


Sa'an nan zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse zan bai wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Zan ba ku ita ta zama mallakarku. Ni ne Ubangiji.’ ”


Amma jama'a suna fama da ƙishirwa, suka yi wa Musa gunaguni. Suka ce, “Don me ka fito da mu daga Masar? Ashe, domin ka kashe mu ne, da mu, da 'ya'yanmu, da dabbobinmu da ƙishi?”


Lokacin da Ubangiji ya bi da mutanensa ta cikin busasshiyar hamada, mai zafi, Ba su sha wahalar ƙishi ba. Ya sa ruwa ya gudano daga cikin dutse dominsu, Ya tsage dutse, ruwa ya kwararo.


Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ