Nehemiya 9:10 - Littafi Mai Tsarki10 Ka kuma aikata alamu da al'ajabai a kan Fir'auna, Da fadawansa duka, da mutanen ƙasarsa, Gama ka san yadda suka yi wa jama'arka danniya. Ta haka ka yi wa kanka suna kamar yadda yake a yau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Ka aika da alamu masu banmamaki da al’ajabai a kan Fir’auna, a kan dukan shugabanninsa da kuma a kan dukan mutanen ƙasarsa, gama ka ga irin danniyar da suka yi wa mutanenka. Ka samo wa kanka suna, wadda ta dawwama har yă zuwa yau. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.