Da yawa daga cikin jama'a suka ba da taimako domin biyan aikin gyaran Haikali. Mai mulki ya ba da zinariya darik dubu (1,000) kwanonin wanke hannu guda hamsin rigunan firistoci ɗari biyar da talatin Shugabannin iyali suka ba da zinariya darik dubu ashirin (20,000) azurfa maina dubu biyu da ɗari biyu (2,200) Sauran jama'a suka ba da zinariya darik dubu ashirin (20,000) azurfa maina dubu biyu (2,000) rigunan firistoci guda sittin da bakwai.