Nehemiya 8:7 - Littafi Mai Tsarki7 Sa'ad da jama'a suke tsaye a wurarensu, sai Lawiyawa, wato su Yeshuwa, da Bani, da Sherebiya, da Yamin, da Akkub, da Shabbetai, da Hodiya, da Ma'aseya, da Kelita, da Azariya, da Yozabad, da Hanan, da Felaya, suka fassara musu dokokin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Lawiyawa, wato, su Yeshuwa, Bani, Sherebiya, Yamin, Akkub, Shabbetai, Hodiya, Ma’asehiya, Kelita, Azariya, Yozabad, Hanan da Felahiya, suka koyar da mutane a cikin Dokar yayinda mutane suke a tsaye a can. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.
Ya kuma faɗa wa Lawiyawa, tsarkakakku na Ubangiji, waɗanda suke koya wa dukan Isra'ila, ya ce, “Ku sa tsattsarkan akwatin alkawari a Haikalin da Sulemanu ɗan Dawuda, Sarkin Isra'ila, ya gina. Ba za ku sāke ɗaukarsa bisa kafaɗunku ba. Yanzu fa sai ku kama hidimar Ubangiji Allahnku da jama'arsa Isra'ila.