Nehemiya 8:5 - Littafi Mai Tsarki5 Ezra kuwa ya buɗe Littafin a gaban jama'a duka, domin yana sama da jama'a. Sa'ad da ya buɗe Littafin, sai jama'a duka suka miƙe tsaye. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20205 Sai Ezra ya buɗe littafin. Dukan mutane kuwa suka gan shi domin yana tsaye a bisa fiye da inda mutane suke tsaye; yayinda ya buɗe littafin kuwa, dukan mutane suka miƙe tsaye. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.