Nehemiya 7:70 - Littafi Mai Tsarki70-72 Da yawa daga cikin jama'a suka ba da taimako domin biyan aikin gyaran Haikali. Mai mulki ya ba da zinariya darik dubu (1,000) kwanonin wanke hannu guda hamsin rigunan firistoci ɗari biyar da talatin Shugabannin iyali suka ba da zinariya darik dubu ashirin (20,000) azurfa maina dubu biyu da ɗari biyu (2,200) Sauran jama'a suka ba da zinariya darik dubu ashirin (20,000) azurfa maina dubu biyu (2,000) rigunan firistoci guda sittin da bakwai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202070 Waɗansu shugabannin iyalai suka ba da kyautai domin taimakon aiki. Gwamna ya ba da darik 1,000 na zinariya, kwanoni 50, da riguna 530 don firistoci. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Huram kuma ya yi tukwanen ƙarfe, da manyan cokula, da daruna. Huram kuwa ya gama dukan aikin da ya alkawarta wa sarki Sulemanu a Haikalin Allah: ginshiƙi biyu dajiya biyu a kan ginshiƙi biyu siffar tukakkiyar sarƙa a kan kowane ginshiƙi Siffar rumman guda ɗari huɗu domin raga don rufe dajiyar ginshiƙan dakali goma daro goma kwatarniya. Bijimi goma sha biyu da suke ɗauke da kwatarniya kwanoni, manyan cokula masu yatsotsi, wato ya yi dukan kayan nan da tagulla domin Haikalin Ubangiji.