Yawan taron jama'a su dubu arba'in da biyu da ɗari uku da sittin (42,360). Barorinsu maza da mata, dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337) Mawaƙa ɗari biyu mata da maza Dawakansu ɗari bakwai da talatin da shida Alfadaransu ɗari biyu da arba'in da biyar Raƙumansu kuma ɗari huɗu da talatin da biyar ne Jakunansu kuwa dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720).