Nehemiya 7:65 - Littafi Mai Tsarki65 Sai mai mulki ya faɗa musu kada su ci abinci mafi tsarki, sai an sami firist wanda zai yi tambaya ta wurin Urim da Tummin tukuna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202065 Sai gwamna ya umarce su kada su ci wani abinci mafi tsarki, sai akwai firist da zai nemi nufin Ubangiji ta wurin Urim da Tummim. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Jimillar waɗanda suka komo duka su dubu arba'in da dubu biyu da ɗari uku da sittin ne (42,360) barorinsu mata da maza, waɗanda yawansu ya kai dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337) mawaƙa ɗari biyu da arba'in da biyar mata da maza dawakansu kuma ɗari bakwai da talatin da shida ne alfadaransu kuma ɗari biyu da arba'in da biyar ne raƙumansu ɗari huɗu da talatin da biyar ne jakunansu dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720)
Da yawa daga cikin jama'a suka ba da taimako domin biyan aikin gyaran Haikali. Mai mulki ya ba da zinariya darik dubu (1,000) kwanonin wanke hannu guda hamsin rigunan firistoci ɗari biyar da talatin Shugabannin iyali suka ba da zinariya darik dubu ashirin (20,000) azurfa maina dubu biyu da ɗari biyu (2,200) Sauran jama'a suka ba da zinariya darik dubu ashirin (20,000) azurfa maina dubu biyu (2,000) rigunan firistoci guda sittin da bakwai.