44 Mawaƙa, na zuriyar Asaf, ɗari da arba'in da takwas.
44 Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 148.
Mawaƙa na zuriyar Asaf, mutum ɗari da ashirin da takwas.
Daga cikin 'ya'yan Asaf, maza, Zakkur, da Yusufu, da Netaniya, da Asharela, Asaf mahaifinsu ne yake bi da su, shi ne kuma mawaƙin sarki.
Lawiyawan da suka komo daga zaman talala, Yeshuwa da Kadmiyel na zuriyar Hodawiya, saba'in da huɗu.
Masu tsaron Haikali su ne zuriyar Shallum, da Ater, da Talmon, da Akkub, da Hatita, da Shobai, ɗari da talatin da takwas.