Sai na yi musu faɗa na la'ance su, na bugi waɗansu daga cikinsu, na ciccire gashin kansu, na sa su rantse da Allah, cewa ba za su aurar da 'ya'yansu mata ga 'ya'yan maza na bare ba, ko kuma su auro wa 'ya'yansu maza 'yan matan bare, ko su auro wa kansu.
Sa'an nan dukan fādawanka za su zo wurina su fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama'arka!’ Sa'an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna a husace.
Sai na yi shawara a zuciyata, na yi wa manya da shugabanni faɗa, na ce musu, “Kuna musguna wa 'yan'uwanku da yake kuna ba su rance da ruwa.” Sa'an nan na kira babban taro saboda su.