Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Nehemiya 4:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Masu ginin garun da masu ɗaukan kaya suna yi da hannu ɗaya, hannu ɗaya kuma na riƙe da makami.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 waɗanda suke ginin katanga. Waɗanda suke ɗaukan kaya suka yi aikinsu da hannu ɗaya, suna kuma riƙe da makami a ɗaya hannun,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Nehemiya 4:17
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Na sha fama, famar gaske, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.


Kai kuma ka jure wa shan wuya, kana amintaccen sojan Almasihu Yesu.


da maganar gaskiya, da kuma ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu.


ba kwa kuwa jin tsoron magabtanku sam. Wannan kuwa ishara ce a gare su ta hallakarsu, ku kuwa ta cetonku, isharar kuwa daga Allah take.


Ku zauna a faɗake, ku dāge ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi.


Don kuwa, an buɗe mini wata hanya mai fāɗi ta yin aiki mai amfani, akwai kuma magabta da yawa.


Da yake waɗansu sun mori halaliyarsu a game da ku, ashe ba mu muka fi cancanta ba? Duk da haka ba mu mori wannan halaliya ba, sai dai muna jure wa kome, don ta koƙaƙa kada mu hana bisharar Almasihu yaɗuwa.


Sai ka sani, ka kuma gane, daga lokacin da aka umarta a sāke gina Urushalima har zuwa lokacin da shugaba, Masiha, zai zo, za a yi shekara arba'in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da kagara.


Saboda haka na sa jama'a su ja ɗamara bisa ga iyalinsu a bayan garu, a wuraren da ba a gina ba. Suna riƙe da takuba, da māsu, da bakuna.


Daga wannan rana, sai rabin barorina suka yi ta gini, rabi kuwa suna riƙe da māsu, da garkuwoyi, da bakuna, da sulke. Shugabannin kuwa suka goyi bayan dukan Yahudawa sosai.


Kowane magini yana rataye da takobinsa sa'ad da yake gini. Mai busa ƙaho yana kusa da ni.


Bari su yi sowa da ƙarfi Sa'ad da suke yabon Allah, da takubansu masu kaifi.


Dukansu gwanayen yaƙi da takobi ne, gogaggu ne na aikin soja, Kowannensu yana da takobi, Suna tsaro don kada a hume su da dare.


Ba ta hawan hanyar juna, Kowa tana bin hanyarta. Takan kutsa cikin abokan gāba, ba a iya tsai da ita.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ