Nehemiya 3:25 - Littafi Mai Tsarki25 Falal ɗan Uzai, ya gyara wani sashi daga kusurwar da hasumiyar benen gidan sarki a wajen shirayin matsara. Bayansa kuma sai Fedaiya ɗan Farosh ya yi gyare-gyare. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202025 sai Falal ɗan Uzai ya yi aiki ɗaura da kusurwa da kuma doguwar hasumiya daga fadar da take bisa kusa da shirayin masu tsaro. Biye da shi, Fedahiya ɗan Farosh အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Zuriyar Farosh, mutum dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172) Zuriyar Shefatiya, mutum ɗari uku da saba'in da biyu Zuriyar Ara, mutum ɗari bakwai da saba'in da biyar Zuriyar Fahat-mowab na zuriyar Yeshuwa da Yowab, mutum dubu biyu da ɗari takwas da goma sha biyu (2,812) Zuriyar Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254) Zuriyar Zattu, mutum ɗari tara da arba'in da biyar Zuriyar Zakkai, mutum ɗari bakwai da sittin Zuriyar Bani, mutum ɗari shida da arba'in da biyu Zuriyar Bebai, mutum ɗari shida da ashirin da uku Zuriyar Azgad, mutum dubu da ɗari biyu da ashirin da biyu (1,222) Zuriyar Adonikam, mutum ɗari shida da sittin da shida Zuriyar Bigwai, mutum dubu biyu da hamsin da shida (2,056) Zuriyar Adin, mutum ɗari huɗu da hamsin da huɗu Zuriyar Ater na Hezekiya, mutum tasa'in da takwas Zuriyar Bezai, mutum ɗari uku da ashirin da uku Zuriyar Yora, mutum ɗari da goma sha biyu Zuriyar Hashum, mutum ɗari biyu da ashirin da uku Zuriyar Gibeyon, mutum tasa'in da biyar.
Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.
Ga jerin iyalan Isra'ila da adadin waɗanda suka komo daga zaman dole iyalin Farosh, dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172) iyalin Shefatiya, ɗari uku da saba'in da biyu iyalin Ara, ɗari shida da hamsin da biyu iyalin Fahat-mowab, wato zuriyar Yeshuwa da Yowab, dubu biyu da ɗari takwas da goma sha takwas (2,818) iyalin Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254) iyalin Zattu, ɗari takwas da arba'in da biyar iyalin Zakkai, ɗari bakwai da sittin iyalin Bani, ɗari shida da arba'in da takwas iyalin Bebai, ɗari shida da ashirin da takwas iyalin Azgad, dubu biyu da ɗari uku da ashirin da biyu (2,322) iyalin Adonikam, ɗari shida da sittin da bakwai iyalin Bigwai, dubu biyu da sittin da bakwai (2,067) iyalin Adin, ɗari shida da hamsin da biyar iyalin Ater (na Hezekiya), tasa'in da takwas iyalin Hashum, ɗari uku da ashirin da takwas iyalin Bezai, ɗari uku da ashirin da huɗu iyalin Yora, ɗari da goma sha biyu iyalin Gibeyon, tasa'in da biyar.